Menu
STARS Project
close
STARS Project
close

Refine your search

STARS Project
Game da mu


STARS aikine na bincike ta hanyar aiki da na’ura mai hango ayukan noma daga sama a Africa ta Yamma Sahara da kuma Asiya ta Kudu. Aikin binciken ya na samun tallafi ne daga kungiyar kasa da kasa ta Bill da Melinda Gates domin tallafa wa kananan manoma akasashe masu fatara.


Gabatarwa- Takala

Kasashe masu karfin tattalin arziki sun samu cin nasara wajen kula da ayyukkan noma ta hanyar kimiya mai amfani da naurar hangen filayen gona daga sama (Remote Sensing). Ayayin da na’urar ta dauki hoton gonakkin noma da kuma kididdiga na irin yanayin kasar noma da kuma yanayin ruwa da ke kwance a kasa da yanayin tudu da tsauni.Wannan kididdgar za a baiwa manoma domin ya amfane su wajen sanin dabarun noma.Wannan aikin na amfani da na’urar bincike da kuma tattaunawa da manoma ta haifar da kyakyawan sakamamako ga manoman ta hanyar girbe amfanin gona mai kyau. Irin wannan dabarar amfani da na’ura na taimakama gwamnati wajen aiwatar da manufofi masu kyau ta haujin aikin gona.
 


Matsalolin gaske da ke addabar kasashen Africa ta yamma ga sahara da kuma kasashen Asiya ta kudu suna takurawa aiki da irin wannan na’urar mai binciken aiyukan gona ta sararin samaniya. Misali kananan manoma da suke noma kashi biyu bisa ukku na abincin duniya suna da filayen noma kankana da kuma filaye masu rashin iyaka da wata gona, kuma suna shukka iraruwan noma daban daban a filin noma daya. Irin wadannan matsaloli sukan sanya na’urar binciken aiyukkan noma ta sararin samaniya ta kasa bada bayanai masu inganci akan harkokin noma a irin wadannan kasashe domin inganta sana’ar noma.

Matsaloli kamar rashin kasar noma mai inganci, cutar da ke addabar shukka, kwarin gona, da kuma fari yana nuna cewa mafi yawan manoma suna shan wahala wajen noma abinci shekara zuwa shekara. A mataki na kasa wadannan matasalolin suna iya haifar da matsalar rashin iya fahimtar yanayin shukka da kuma ciyawa, samun kai albakar noma a kasuwa. An samu kuskure da yawa wajen daukar mataki akan cewa ko ya kamata a sayo abinci daga kasashen waje domin a rage gibin da ake samu a kowace shekara akan abinda manoma suka noma. Akwai misalai a inda aka shigo da kayan abinci  akan kuskure sai gashi kuma a wannan shekarar an samu amfanin gona mai yawa , wanda ya haifar da yawan abinci a kasuwa da ya sanya manoma a wannan shekarar suka fuskanci faduwar farashin amfanin gona.