Menu
STARS Project
close
STARS Project
close

Refine your search

STARS Project
Game da mu

Amfani

Idan za a iya samar da hanyoyin amfani da na’urar bincike ta sararin samaniya a kasashen Africa ta yamma ga Sahara da kuma Asiya ta kudu kamar haka:

  • Kananan manoma za su iya samun karin bayani mai haske, wanda zai basu damar su iya zartar da hukunci akan abinda zasu noma da kuma yanda za su shukka wadannan irarurwa, wanan zai iya sa a samu amfanin gona mai yawa da kuma karuwar arziki ga manoma  masu karamin karfi a kasashe matalauta.
  • Za a samu cikakken bayani akan iraruwa da kuma yanayin kasar noma wanda zai baiwa kananan manoma da kuma karkarar su samun damar mallakar fili a hukumance. Saboda sau da yawa manoma ke rasa filayen noman su.
  • STARS yazo ne ba tare da biyan kudi daga kananan manoma ba kuma da anniyar bayar da ilmi da horarsuwa domin amfanin manoma. Haka kuma zai bada damar fadada aiyukkan amfani da na’urar binciken aikin gona ta sararin samaaniya.
  • Haka kuma, kasashen masu karamin tattalin arziki zasu samu damar iya hango yanda zasu sarrafa amfanin gonarsu a matakin kasa domin samar da abinci ga yawan al’ummarsu.
  • Yanayin sarrafa abinci a kasahen masu tasowa zai amfani manoma a kasuwa domin za su iya noma iraruwa masu bada amfani mai yawa. Za a samu damar fitar da kayan amfanin gona a kasashen waje domin tallafa ma arzikin kasa.

Manufar STARS shine binciko ko da amfani da na’urar bincike ta sararin samaniya zata iya kawo irin wadannan amfani, kuma a samu karin yawan samar da abinci a kasahen masu tasowa.