Menu
STARS Project
close
STARS Project
close

Refine your search

STARS Project
Game da mu

Aikin STARS

Wananan bincike na STARS zai fara aiki ne a daya ga watan Yuni na shekarar 2014. Aikin STARS an kirkiro shi ne domin bincike akan hanyoyin da za a iya magance matsalolin da aka ambata a baya. Sashen kimiyar kasa da labarai na Jami’ar TWENTE a kasar Nezaland ke jagorancin hadin guiwar masana akan harkar binciken aikin gona ta amfani da na’urar a sararin samaniya domin tantance wane irin bincike ne zai haifar da amfani mai yawa a tsawon rayuwar aikin STARS na wata ashirin.

 Hadin guiwar ya kunshi kungiyoyin masanan bincike  na duniya kamar haka:

  • Kungiyar taron kasashen mulkar Ingila mai binciken harkokin masana’antu ta kasar Australia;
  • Kungiyar duniya ta harkokin binciken iraruwa da ke kasashe masu zafi a kasar Mali da kuma Najeriya;
  • Jami’ar Meriland ta kasar Amurka da ke Tanzaniya da Uganda;
  • Kungiyar duniya mai binciken hanyoyin inganta noman masara da alkama da ke kasar Bangaladash da kuma Mekzico.