Menu
STARS Project
close
STARS Project
close

Refine your search

STARS Project
Game da mu

Mabanbancin yanayin guraren bincike

Aikin kungiyar STARS yana da hanyoyin bincike guda ukku:

  • Akasashen Mali da Nijeriya ana bincike akan yanayin amfani da filayen noma a karkara ashirin tare da manoma dari da hamsin domin fito da hanyoyin shawarwari ga kananan manoma.
  • A kasar Tanzania da Uganda, STARS tare da hadin kan wasu kungiyoyin duniya na kula da wasu makeken filayen noma guda hudu domin bincike akan samar da abinci.
  • Aiki na ukku yana kasar Bangaladash, a inda na’urar bincike ta sararin samaniya ke bada bayanai akan filin kasa dake bangaren Bengel Delta domin tantace ko manoma za’a iya barinsu su yi amfani da ruwan rani domin noma.


Kari ne ga kokarin da shiyoyin bincike da cibiyoyin nazarin filayen noma ta hanyar amfani da na’urorin da sanya hannun jari don gano mafari a bayanan harkan noma inda na’urorin kan iya taimakawa dan bunkasa cigaban harkan noma. Sa’anan, zai sake bada haske wurin sa jari nan gaba da kuma hanyoyin da za’a yi haka. Bincike na yanayin kasar noma yayi nazarine sosai akan tunanin da ke da dangantaka da wadannan gwaje gwajen da aka yi na shiyoyin bincike tare da la’akari da dukkan masu ruwa da tsaki da kuma fasahar harkan noma.